Talata 9 Yuni 2026 - 21:31
Dalilan Da Suka Kawo Taɓarɓarewar Kasashen Musulmi A Mahangar Imam Khumaini (R.A)

Hauza/ Tsayawa wuri guda da baya-bayan nan da ake samu a ƙasashen musulmi, ba wai wata ƙaddara ce da ba za a iya kauce mata ba, a'a, wata matsala ce da ta samo asali daga rabe-raben da aka samu tsakanin gaskiyar addini da kuma zahirin yanayin rayuwa. Domin tsallake wannan dambarwa ta tarihi, da farko dole ne a binciko tushen dalilan cikin gida da na waje da suka haddasa koma bayan ƙasashen musulmi, sannan a nemo hanyoyin fita daga cikinta. Wannan babban al'amari kuwa zai fito fili ne ta hanyar zurfafa tunani a kan ra'ayoyin Imam Khumaini.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya bayar da rahoton cewa sanin dalilan baya-bayan nan na ƙasashen musulmi ya kasance abin damuwa na bai-daya ga masu neman gyara na wannan zamanin. Sai dai a tunanin Imam Khumaini, wannan batu ya wuce nazari na tattalin arziki ko siyasa kawai, yana da tushe mai zurfi a cikin al'adu da amincewa da kai. Yayin da yake bayani filla-filla kan abin da ke kawo cikas ga ci gaba, ya yi amon cewa muddin ba a gyara gurbataccen tunani da dogaro ga wasu ta fuskar tunani ba, babu wani sauyin siyasa da zai kai ga daukaka mai dorewa.

Wannan rubutu — wanda ya dogara da bayanan littafin "Dalilan Koma Baya da Rashin Ci Gaban Kasashen Musulmi a Mahangar Imam Khumaini da Ayatullah Khamenei" da cibiyar bincike ta juyin juya halin Musulunci ta wallafa — yana kokarin sake duba tsarin tunanin Imam Khumaini, tare da bayyana tushen dalilan cikin gida da na waje na koma bayan da kasashen musulmi ke ciki, sannan ya zana taswirar fita daga wannan dambarwa ta tarihi bisa ginshikin farkawar Musulunci da haɗin kai.

A) Dalilan Cikin Gida Na Tabarbarewa

1. Gurɓatattun Al'adu

A cikin nazarin tunanin Imam Khumaini, ga alama ma'anar "gurɓatattun al'adu" a cikin abubuwan cikin gida da kuma ma'anar "mulkin mallaka" a cikin abubuwan waje, su ne mafi muhimmancin shika-shikan ma'ana a cikin tsarin ra'ayinsa game da dalilan rashin ci gaba da koma bayan ƙasashen musulmi. Domin bayanansa a kan wadannan fannoni guda biyu suna mayar da dalilin koma bayan zuwa gare su ta fuskoki daban-daban.

Kodayake kalmar "gurbatattun al'adu" ba ta fito fili kai tsaye a cikin maganganunsa ba, amma abubuwan da ke cikin tunanin Imam a kan ci gaba da rashin ci gaba suna nuni ne ga shawarwarin da ke ganin tushen koma bayan shi ne gurbataccen tunani na musulmi, wanda shi da kansa ya kira shi da "Mu'avvaj" (karkatacce). Wani tunani ne da ya fito a matsayin al'adun gama gari a cikin sassa daban-daban na al'umma, wanda ya juyar da fannonin tunani da na kimiyya na ci gaba da ɗaukaka. A zahiri, bisa ga abubuwan da ke cikin kalaman Imam Khumaini, gurɓatattun al'adu su ne silar matsalolin cikin gida da duniyar musulmi ke fama da su.

A mahangar Imam Khumaini, al'adun musulmi saboda karkacewa daga ma'aunin da ake kira al'adun Musulunci, suna rayuwa ne a cikin tsanani da koma bayan rayuwa. Tunanin Imam na addini yana kallon al'adun Musulunci ko kuma hanya madaidaciya a matsayin hanyar Annabawa musamman Annabin Musulunci (S.A.W.A), kuma yana siffanta waninta, gami da al'adun yammacin duniya da na mulkin mallaka, a matsayin karkatattu. A cewar Imam, al'adu da tunanin da ke gudanar da rayuwar musulmi sun karkace daga tafarkin Musulunci da abubuwan da ke gina wayewar kai, wanda hakan ya sanya al'ummomin musulmi cikin bacci na gafala, kasala, ragwanta da kuma daskarewar tunani.

2. Gwamnatoci Masu Ci Baya

A mahangar Imam, gwamnatin ƙasashen musulmi saboda dalilai daban-daban suna taka muhimmiyar rawa wajen taɓarɓarewa da koma bayan ƙasashen musulmi. Ma'ana, tsirarun da ke mulki a kan tsarin siyasa na kama-karya da rashin ci gaba, sun hana al'ummomin musulmi ɗaukaka da ci gaba. A cikin wannan tsari, ya ba da fifiko na musamman ga gurɓataccen yanayi na cikin gida na jami'an gwamnati, kamar kaucewa adalci, sha'awar zama a gidajen sarauta, kwadayin duniya da son kai.

Wani bangare na wannan taɓarɓarewar yana komawa ne ga tsohon tsarin siyasa mai ci baya a ƙasashen musulmi. A mahangar Imam, tsarin sarauta shi ne tushen koma bayan rayuwa da rashin sa'ar al'ummomi; domin tsarin mulkin mallaka da na sarauta saboda hana al'umma zaɓar abin da suke so, naɗa jami'ai marasa cancanta, da gudanar da mulki ta hanyar firgitarwa da karfi; suna da tsohon tsari da ya ruɓe, kuma irin wadannan karkatattun tsare-tsare ba za su iya zama masu jagorantar al'ummarsu zuwa ga ci gaba ba.

3. Malaman Addini Masu Halin Ko-In-Kula

Imam Khumaini, a cikin abubuwan da ke kai al'ummar musulmi ga taɓarɓarewa, ya mayar da hankali na musamman ga rawar da malamai da masana addini ke takawa wajen zurfafa koma bayan al'ummomin musulmi. Mafi muhimmancin matsalar Imam a kan wannan batu ita ce rashin sha'awar malamai wajen shiga cikin al'amuran siyasa da na al'umma. A mahangar sa, shigar malamai cikin siyasa yana nufin kula da makomar al'umma da kuma nuna damuwa ga al'amuran zamantakewa, tattalin arziki da al'adu na al'ummomin musulmi. Sai dai abin da ya kawo cikas ga wannan halartar da kula a cikin shekarun baya shi ne dasa ra'ayin cewa ya kamata malamai su koma lungunan makarantu da masallatai kawai.

Ta haka ne keɓewa da halin ko-in-kula na madugun al'umma da misalan zamantakewa musamman malamai a cikin al'ummar Musulunci, da rashin damuwarsu kan makoma da matsalolin al'ummar Musulunci ke bazuwa zuwa ga talakawa, yana mai da su marasa damuwa wajen magance matsaloli da koma bayan nan da ake ciki. A mahangar Imam Khumaini, amon cewa malamai da addini da siyasa a rabe suke, sannan kuma rashin nuna damuwa ga makomar musulmi da kuma yin shiru a kai; ya mamaye tunanin wasu malaman Musulunci ta yadda yanzu shiga siyasar ake kallonta a matsayin abin ƙyama da aikin assha.

4. Masanan Zamani Masu Dogaro Ga Waje 

Rawar da masanan zamani wato masu tunani da ilimi ke takawa wajen sauye-sauyen tunani da na zahiri na al'umma abin ne da ba za a iya musanta shi ba. A mahangar Imam Khumaini, masanan zamani a gungun su guda biyu; masana masu addini da kuma wadanda suka kamu da cutar yammacin duniya (masu ɗaukar tunanin yammaci), sun kasance tushen sauye-sauye masu kyau da marasa kyau a duniyar musulmi. Ta yadda a cikin bayanansa, daya daga cikin dalilan taɓarɓarewa da koma bayan al'ummar Musulunci daga samun ci gaba mai daukaka shi ne kasancewar masana na zamani masu dogaro ga gabas da yamma, wadanda tare da nisanta kansu da tsarin ƙasarsu da rashin sanin ka'idojin da ke gudanar da rayuwar al'ummomin musulmi; ba su da cikakken sani kan dokoki masu daukaka na addinin Musulunci.

A mahangar Imam, dogaro na tunani da al'adu na masanan zamani ga tsarin gabas da yamma, da kuma bacewar kai a gaban alamomin wayewar kai na waje; yana sanya su yin watsi da damar al'adu da na zahiri da na dabi'a da ake da su, sannan kuma suna ƙasƙantar da kayan tarihi na zahiri da na ruhaniya na kasa; ta yadda duk wani riko da al'adun gida ake fassara shi da koma bayan rayuwa da tsohuwar al'ada.

5. Raunin Hadin Kan Cikin Gida

Imam ya bayyana cewa daya daga cikin ginshikan shan kashi da koma bayan al'ummomin musulmi shi ne saɓani, rarrabuwa da rashin haɗin kan cikin gida. A ra'ayinsa, iyakoki daban-daban na jam'iyyu, ƙabilanci da na aƙida suna haifar da rikice-rikice da saɓani da ke kai al'umma da gwamnati ga taɓarɓarewa, kuma a cikin irin wannan yanayi ba za a iya tsammanin yanke shawara na bai-daya da bin diddiginsa bisa amfanin al'umma gaba daya ba; don haka Imam ya bukaci masu wa'azi da su kira mutane zuwa ga haɗin kan kalma, ci gaba da yunkuri, tsoron Allah da hakuri na juyin juya hali, kuma su tsoratar da su daga saɓani da rarrabuwa — wanda shi ne tushen shan kashi da koma bayan rayuwa. A kalaman Imam, a saman dukkan gurɓacewa da lalacewa akwai rarrabuwa da saɓani da ke hawa kan son zuciyar dan adam da al'ummomi domin kai su ga halaka. A takaice, saɓani da rarrabuwa sune hanyar da maƙiya Musulunci da baƙi ke bi wajen mamaye al'amuran kasashen musulmi.

6. Rashin Hadin Kan Musulmi 

Bambance-bambancen ɓangaranci da ra'ayoyin son kai na cikin gida da sunan Shi'a da Sunna da kuma saɓanin ƙabilanci a ra'ayin Imam Khumaini wata annoba ce da ta ninka matsalolin musulmi. Yayin da kiran Annabawa ya kasance a kan tsarin haɗin kai da yin riko da "Hablullah" (igiyar Allah), kuma an bukaci musulmi da kada su rarraba daga wannan igiya mai karfi. Tabbatar da wannan babban al'amari a mahangar Imam yana bukatar aiki da gaske da himma ta dukkan shugabannin al'umma, manyan malamai na garuruwa da masana domin tabbatar da haɗin kai tsakanin al'ummomin musulmi. Ya jaddada cewa matsalolin ƙasashen musulmi za su iya warwarewa ne kawai da hannunsu. Sai dai abin da ya shagaltar da su daga batun haɗin kai a mataki na farko shi ne gafala da nisantar musulmi da Musulunci na gaskiya. A ra'ayinsa, musulmi a bangare guda saboda rashin fahimtar Musulunci daidai, da takaita shi a cikin hukunce-hukunce na ibada da addu'o'i da sauran su, sun nutsar da kansu cikin gurɓatattun aƙidu da camfi, a ɓangare guda kuma ta hanyar fifita abubuwan da ke kawo saɓani tsakanin bangarorin addini da kuma rufe ido ga asalin addinin Musulunci, sun tashi tsaye wajen lalata kansu da Musulunci.

Rarrabuwa da dambarwar kasashen musulmi ita ce hanya da tashar da kasashen mulkin mallaka ta hanyar haɗin gwiwa da macizai maciya amana da shugabannin sulhu na ƙasashen musulmi ke kwashe dukiyar al'ummomin musulmi. Yayin da ɗaukakar duniyar musulmi a shekarun baya ta kai su ga kololuwar ɗaukaka da wayewar kai; rarrabuwa da fuskoki daban-daban sun janyo su daga kololuwar girma zuwa yanayin da ake ciki yanzu domin albarkatun kasa da na tattalin arziki sun fada cikin aljihun baƙi cikin sauki.

B) Dalilan Waje Na Taɓarɓarewa 

1. Mulkin Mallaka 

Mulkin mallaka a tsawon kasancewarsa a yankin Gabas ta Tsakiya da duniyar musulmi wato tun farkon karni na sha shida miladiyya da siffofinsa na da da na yanzu tare da haɗewa da kafafen yaɗa labarai da na sadarwa, a koyaushe yana kokarin gudanar da tsarin ci gaba a waɗannan kasashe ta hanyoyin daban-daban domin amfanin ƙasashen yamma, kuma wannan tsari yana karbe wadancan muhimman abubuwa na ci gaba wato al'adu, dukiya da gwamnati da mai da su daidai da manufofin mulkin mallaka. Kasancewar yawancin ƙasashen musulmi a manyan hanyoyin dabarun yaki (Strategic) da mallakar manyan albarkatun mai da iskar gas, ya sanya duniyar musulmi ta kasance ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin mulkin mallaka a shekarun baya.

Sakamakon irin wannan kasancewar shi ne kafa gwamnatoci masu dogaro da na 'yan koren da ke karkata ga yammacin duniya, rugujewar daular Usmaniyya da kafa tsarin siyasa bisa maslahar ƙasashen mulkin mallaka, da kafa cibiyoyin rikici na dindindin na ƙabilanci da na addini tare da kafa gwamnatin mamaya ta Kudus (Isra'ila), wanda hakan a koyaushe yana janye kuzari, lokaci da ƙarfin al'ummomi daga gine-gine da ci gaba da ya dace da al'ummomin musulmi, yana mai da shi zuwa ga rikice-rikice da faɗace-faɗace na cikin gida.

Nazari a cikin bayanai da tunanin Imam yana nuna cewa a cikin abubuwan waje, abu guda kuma mafi mahimmanci da ya sanya ƙasashen musulmi nisanta da koma bayan rayuwa daga ɗaukaka da ci gaba bisa bukatun gida da dokokin Musulunci, shi ne mulkin mallaka. Babu shakka mahangar abubuwan duniya da ke gudanar da rayuwar masu mulkin mallaka na gabas da yamma ita ce kaiwa ga matsakaicin riba ta duniya ta hanyar amfani da albarkatun kasa da na ɗan adam. A mahangar Imam, masu mulkin mallaka a shekarun baya saboda bincike na yanayin rayuwar mutane sun san halaye da ka'idojin duniyar musulmi da kyau, kuma mafi muhimmancin hanyar da za su iya samun matsakaiciyar riba ita ce sauya aƙidun da ke da alaka da ci gaba zuwa ga gurɓatattun al'adu da tunani maras amfani.

A kalaman Imam, mamayar al'adu ko kuma al'adun mulkin mallaka ta hanyar haifar da "ƙirƙirarren bacci", ta jagoranci tunanin musulmi ta yadda aka karɓe musu damar yin tunani kan maslaha da matsalolin duniyar musulmi. Babban buri a cikin wannan salon na mulkin mallaka shi ne hana horar da mutane masu amfani ga ci gaba, hana aiwatar da hukunce-hukuncen Musulunci wajen ci gaba da daukaka, kuma a karshe horar da mutane masu gurɓataccen tunani da ke goyon bayan gabas ko yamma waɗanda da mafi karancin kudi ke bin manufofin mulkin mallaka a kasashensu.

Hanyoyin Fita Daga Taɓarɓarewa 

1. Riko Da Musulunci

Tunanin addini na Imam Khumaini yana ganin hanyar magance yawancin matsaloli tana cikin riko da koyarwar addinin Musulunci; domin ya yi amon cewa Musulunci shi ne mai ceto ɗan adam daga dukkan fannonin koma bayan rayuwa. Imam yana kallon Musulunci a matsayin wani tsari na bai-daya, cikakke kuma mai fuskoki daban-daban wanda ke da cikakken iko a kan dukkan al'amuran mutum na kansa da na al'umma ko ta fuskar zahiri ko ta baɗini, kuma ya sanya doka domin gudanar da shi.

2. Juyin Juya Halin Siyasa Da Gyare-Gyare Na Asali

Tunda yake gwamnatoci masu ci baya da na kama-karya babban shinge ne a gaban gyara matsaloli da koma bayan duniyar musulmi, juyin juya hali da rusa tsarin siyasa maras maraba da mutane kuma mai yaƙi da Musulunci shi ne matakin farko na shiga tafarkin ɗaukaka da ci gaba. A lokaci guda, a mahangar sa, dukkan matsaloli da koma bayan rayuwa ba za su warware da juyin juya halin siyasa kawai ba, kuma bayan haka ci gaba zai yiwu ne ta hanyar gyare-gyare; domin sauya gurɓatattun al'adu da tunanin da ya gurɓace da son yammacin duniya ba abu ne da za a iya gudanar da shi lokaci guda zuwa ga ɗaukaka ba.

3. Shiga Tsakani Mai Kyau Da Wayewa

Imam a koyaushe yana jaddada shiga tsakani mai kyau da wayewa na sassa daban-daban na mutane a fagen zamantakewar siyasa domin su fita daga kasala da ko-in kula, kuma su kasance masu damuwa da matsalolin al'ummar Musulunci da sauran kasashen musulmi, kuma su dauki mataki na bai-daya tare da tsarin haɗin kai wajen magance su. Misali, a mahangar Imam, raunin wannan rashin sanya ido da shiga tsakani daga al'umma da madugun zamantakewa yana haifar da lalacewa da gurbacewa, don haka kare Musulunci da rashin karkacewar gwamnati ya dogara ne da kasancewa a fagage daban-daban na siyasa da na zamantakewa.

4. 'Yancin Tunani Da Na Al'adu

A cikin tunanin Imam, 'yancin al'adu da na tunani yana da matsayi na musamman, kuma tare da jaddada 'yancin al'adu da na tunani daga sauran al'adu masu kawo farmaki da na mulkin mallaka, yana jaddada dawo da al'adun gida da na Musulunci a cikin al'ummomin musulmi, ta yadda ya sanya juyin juya halin Musulunci na Iran a cikin tsarin cimma wannan buri. Shawarwarinsa na akai-akai kan gina al'adu masu zaman kansu kuma ba shakka masu moriyar al'adu masu arziki na Musulunci a koyaushe suna tafiya tare da gargadi game da farmaki mai fadi na al'adun yammacin duniya; domin ya ambata cewa al'adun mulkin mallaka na iya tasiri ga kasancewar al'adun Musulunci kuma su rage shi a rayuwar musulmi ta kashin kai da ta al'umma.

5. Horar Da Mutane Masu Amincewa Da Kai Da Kuma Sauke Nauyi

A mahangar Imam, iyali kuma a saman sa mata saboda rawar tarbiyya da gina ɗan adam, suna taka muhimmiyar rawa da ɗaukaka wajen faduwa da ci gaban al'ummomi, kuma suna iya nisantar da al'umma daga faɗawa cikin taɓarɓarewa ta hanyar rainon tsara mai wayewa da jaruntaka. A cewar Imam, mallakar ruhin gine-gine da bunkasa ƙasa gami da sha'awa da son aiki tare da sauke nauyi na iya biyan koma bayan nan da ake ciki. Gaba daya Imam yana ganin daukaka da ci gaba sun ta'allaka ne da sauke nauyi da sanin ya kamata, ta yadda kowa a kowane matsayi da kwarewa yake ya shagala da gudanar da ayyukansa cikin sha'awa.

6. Hadin Kai Da Jituwa Ta Cikin Gida

A koyaushe Imam Khumaini ya kasance yana jaddada batun gina al'umma (Umat) da kuma karfafa jituwa da haɗin kan cikin gida na al'ummar Musulunci tare da iyakokin da suka haɗa duniyar musulmi gaba daya, kuma ya ambaci cewa sirrin nasara da yin galaba a kan danniya, kwashe dukiya da koma bayan rayuwa shi ne haifar da kuma kare haɗin kai, jituwa da daidaiton tunani tsakanin musulmi. Ya faɗi cewa da hadin kan kalma tsakanin gwamnatocin musulmi, tsammanin magance matsaloli da dambarwar duniyar musulmi abu ne mai kyau; za su iya sanya zukatan al'ummominsu su karkata zuwa ga al'ummar Musulunci baki daya.

7. Yada Wayewar Kai Da Farkawar Musulunci

Imam ya sha jaddada bukatar farkar da sauran musulmi ta hannun mutane masu ra'ayin juyin juya hali da wayewa musamman malaman Musulunci. Nuna dalilan koma bayan rayuwa da taɓarɓarewa, sannan da kwaɗaitar da su wajen yaƙi da kama-karya da mulkin mallaka, da janyo zukatansu zuwa ga Musulunci na gaskiya da haɗin kai; abubuwa ne da aka tabbatar da misalinsu a juyin juya halin Musulunci na Iran, kuma yana sha'awar cewa waɗannan abubuwa da nufin magance matsalolin duniyar musulmi, su bazu kuma a bayyana su a cikin sauran kasashen Musulunci.

Madogara:

Mehrabi Koshki, Raziya (1400). Dalilan Koma Bayan Kasashen Musulmi a Mahangar Imam Khumaini da Ayatullah Khamenei, Wallafa ta Farko, Tehran: Cibiyar Bincike ta Juyin Juya Halin Musulunci, shafuka 86-145

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha